IQNA

Wasu Daga Cikin Kasashen Musulmi Sun Yi Allawadai Da Kisan Musulmi A Myanmar

17:48 - July 21, 2012
Lambar Labari: 2373889
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin kasashen musulmi sun fito sun yi kaakusar suka kan kisan kiyashin da ake yi wa musulmi a kasar Myanmar acikin ‘yan lokutanan kasantuwarsu marassa rinjaye a kasar kamar dai yadda wasu kafofin yada labarai suka tabbatar duk kywa da irin goyion bayan da mahukuntan kasar suke samu kan wannan mataki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WAM cewa, wasu daga cikin kasashen musulmi sun fito sun yi kaakusar suka kan kisan kiyashin da ake yi wa musulmi a kasar Myanmar acikin ‘yan lokutanan kasantuwarsu marassa rinjaye a kasar kamar dai yadda wasu kafofin yada labarai suka tabbatar duk kywa da irin goyion bayan da mahukuntan kasar suke samu kan wannan mataki daga kasashen yammacin turai.
Tsohon shugaban hukumar ayyukan leken asirin kasar Masar wato Umar Suleiman ya mutu a safiyar yau, Kamfanin dillancin labaran kasar ta Masar ya ce Suleiman ya mutu ne a hannun likitoci a wani asibitin da ke Amurka a daidai lokacin da suke duba lafiyarsa, to sai dai wani na hannun damar Umar Suleman mai suna Hussain Kamal, ya ce tsohon shugaban hukumar leken asirin ya je asibitin ne a cikin koshin lafiya.
Umar Suleman dai ya kasance babban kusa a tsohuwar gwamnatin Husni Mubarak, sannnan a matsayinsa na shugaban hukumar leken asiri, ya kasance babban amini ga Amurka da kuma Isra'ila, sannan kuma Mubarak ya nada shi a matsayin shugaban riko na kasar a lokacin da boren al'ummar kasar ya tilasta masa sauka daga kan mukaminsa a cikin shekarar bara.
1057724



captcha