Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na press TV jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka dangane da yadda kasashen duniya suka shiri da bakunansu kan kisan gilla da kuma cin zarafin da ake yi wa mabiya addinin mulunci a kasar Myanmar da suke fuskantar za,unci tare da cikakken goyon bayan kasashen yammacin turai da suke raya kare hakkin bil adama a duniya, amma a halin yanzu sun manata da hakan.
Kamar yadda ake tsammani, kasahen Rasha da China sun hau kan kujerar naki ko kuma abinda ake kira veto dangane da bukatar da kasashen yamma suka gabatar a komitin tsaro na MDD kan kara takurawa gwamnatin shugaba Bashar Al-asad na kasar Syria, a jiya Alhamis ne mambibin komitin tsaro na MDD 15 suka kada kuri'a a kan wannan bukatar, inda kasashe 11 suka amince da kudurin, ukku daga cikinsu masu kujerun din din din a komitin ne, wato kasashen Amurka Faransa da kuma Britania, a yayinda kasashe biyu masu kujerun din din din a komitin wato Rasha da China kuma suka ki amincewa da kudurin, sannan kasahen Pakistan da kuma Afrika ta kudu, wadanda membobin komitin ne na wucin gadi, sun kauracewa kada kuri'ar.
Tare da wanna matsayin da kasashen Rasha da kuma china suka dauka, kokarin da kasashen yamma tare da wasu kawayensu a kasashen larabawa na kara takurawa gwamnatin kasar Syria ya kasa kai labari.
Sa'o'ee kadan, kafin a fara kada kuri'a kan wannan bukatar a komitin, shugaban kasar Amurka Barak Obama ya kira tokwaransa na kasar Rasha Vlidemir Putin ta wayar tarho inda ya yi kokarin gamsar da shugaban na kasar Rasha kan bukatar amincewa da wannan kudirin.
Kasashen Rasha da China dai sun bayyana cewa kudurin da kasashen yamma suka gabatar yana nuna goyan baya ga bangare guda ne cikin bangarorin da suke riciki a kasar ta Syria, wato yan tawayen kasar, wadanda kuma suka dauke da makamai kuma suke samun tallafi daga wadannan kasashe.
Jakadan kasar Rasha a komitin, ya kara da cewa, kudirin ya yi hannun riga da yarjejeniyar Geneva ta warware rikicin kasar Syria ta hanyar tattaunawa, har'ila yau bukatar ta yi watsi da shawarar Kofi Annan, tsohon babban sakatarin MDD, kan warware rikicin na kasar Syria, mai bukatu.
1057671