IQNA

An Bude Cibiyar Ilimi Ta Mabiya Mazhabar Shi’a A Kasar Masar Karon Farko

17:48 - July 21, 2012
Lambar Labari: 2373894
Bagaren kasa da kasa, an kafa babbar makaranta ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Masar wanda hakan shi ne karon farko da suka samu wannan damar da ak aharamta musu a lokacin kama karya da fir’anaci na tsohon shugaban kasar Husni Mubarak aminin kasashen yamma.
Kamfanin dillanin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an kafa babbar makaranta ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Masar wanda hakan shi ne karon farko da suka samu wannan damar da ak aharamta musu a lokacin kama karya da fir’anaci na tsohon shugaban kasar Husni Mubarak aminin kasashen yamma da kuma haramtacciyar gwamnatin yahudawa.
Tsohon shugaban hukumar ayyukan leken asirin kasar Masar wato Umar Suleiman ya mutu a safiyar yau, Kamfanin dillancin labaran kasar ta Masar ya ce Suleiman ya mutu ne a hannun likitoci a wani asibitin da ke Amurka a daidai lokacin da suke duba lafiyarsa, to sai dai wani na hannun damar Umar Suleman mai suna Hussain Kamal, ya ce tsohon shugaban hukumar leken asirin ya je asibitin ne a cikin koshin lafiya.

Umar Suleman dai ya kasance babban kusa a tsohuwar gwamnatin Husni Mubarak, sannnan a matsayinsa na shugaban hukumar leken asiri, ya kasance babban amini ga Amurka da kuma Isra'ila, sannan kuma Mubarak ya nada shi a matsayin shugaban riko na kasar a lokacin da boren al'ummar kasar ya tilasta masa sauka daga kan mukaminsa a cikin shekarar bara.

Wasu masu bin diddigin lamurran da suke faruwa na siyasar kasashen larabawa sun imanin cewa, Muhammad Mursi yana da babban kalu bale a gabansa, kasantuwar cewa da dama daga cikin mutanen da suka jefa masa kuri'a suna da fatan ganin ya yanke alakar kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da taimaka ma al'ummar palastinu, sabanin gwamnatin Husni Mubarak da ta kasance babbar kawa ga Isra'ila, da ake hada baki da ita wajen cutar da al'ummar palastinawa.
Bugu da kari kan hakan, wasu daga cikin kasashen larabawa da suke dasawa da Amurka kuma suke kare manufofinta a cikin kasashen larabawa da na musulmi a halin yanzu kamar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa, ba su lale marhabin da zabar Mursi a matsayin shugaban kasar Masar ba, domin kuwa sun yi iyakacin kokarinsu wajen kasha biliyoyin kudade domin muguda sakamakon zaben na kasar Masar da nufin kayar da Mursi amma hakan bai kai ga nasara ba, wannan ne ma ya sanya Mursi yake kokarin tabbatarwa irin wadannan kasashen larabawa da cewa ba zai mayar da hankali kan abubuwan da suka faru ba, maimakon haka yana neman hadin kansu domin tunkarar gaba.
Yanzu dai za a iya cewa kasashen Amurka da sauran kawayenta larabawa musamman Saudiyya, suna baiwa Mursi rata ne domin su ga kamun luddayinsa, idan har zai iya tafiya da salon siyasa da zai kare manufofinsu, ko da kuwa bai kai kamar yadda babban aminsu Husni Mubarak ya kasance yanayi ba, to za su iya daga masa kafa, a matsayin rashin uwa a kan yi uwa daki.
1057644




captcha