IQNA

Cibiyar Kusanto Da Mazhabobin Muslunci Ta Mika Sakon Ta’aziyyar Samir Sulaiman

11:56 - July 22, 2012
Lambar Labari: 2374426
Bangaren siyasa, cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci ta aike da sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan Samir Sulaiman na kasar Lebanon wanda daya ne daga cikin fitattun mambobin wannan cibiya wanda Allah ya yi masa rasuwa a cikin makon nan da muke ciki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na cibiyar taqrib cewa cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci ta aike da sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan Samir Sulaiman na kasar Lebanon wanda daya ne daga cikin fitattun mambobin wannan cibiya wanda Allah ya yi masa rasuwa a cikin makon nan da muke ciki, wanda kuma daya ne daga cikin masu goyon bayan gwagwarmayar Musulunci a kasar tare da bada dukkanin gudunmawar da yake iyawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya tana gudanar da muhimman ayyukanta ne tare da hadin gwiwa da cibiyoyin Musulunci daga sassa na duniyar musulmi, da nufin tabbatar da cewa an kusanto da fahimtar mabiya addinin muslunci da kuma kauce ma abin da makiya wannan addini suke kokarin dasawa a tsakanin al’ummar da nufin rarra kawunansu domin tabbatar da manufofinsu na keta kan wannan al’umma.
Cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci ta aike da sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan Samir Sulaiman na kasar Lebanon wanda daya ne daga cikin fitattun mambobin wannan cibiya wanda Allah ya yi masa rasuwa a cikin makon nan da muke ciki, kuma tuni iyalansa suka ci gaba da karbar ta’aziyya daga sauran muuslmi da masana daga sassan duniya.
1058443



captcha