IQNA

Dole Ne Amurka Ta Tabbatar Da Cewa Tana Mutunta ‘Yancin Iran A Aikace

11:56 - July 22, 2012
Lambar Labari: 2374429
Bangaren siyasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa idan kasar Amurka tana son tabbatar wa duniya cewa tana mutunta ‘yancin kasashen duniya tare da kare hakkokinsu to ya zama wajibi kanta ta mutunta ‘yanci jamhuriyar muslunci ta Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa idan kasar Amurka tana son tabbatar wa duniya cewa tana mutunta ‘yancin kasashen duniya tare da kare hakkokinsu to ya zama wajibi kanta ta mutunta ‘yanci jamhuriyar muslunci ta Iran a matsayin kasa mai cikakken iko da cin gashin kanta, maimakon kokarin tilasta salon siyasarta ta zalunci da danniya kanta da sauran matakai na zalunci ga al’ummar kasar.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar CBS din, Dan Raviv ya bayyana cewar a cikin kungiyar leken asirin akwai wani bangare da aka ware da aka ba su aikin kashe masanan nukiliyan Iran. Har ila yau a cikin wannan littafin, marubucin ya yi ishara da wasu daga cikin ayyukan ta'addanci da kisan gilla da kungiyar din ta aikata a biranen Beirut da Damaskus na kasashen Labanon da Siriya inda yake cewa a halin yanzu 'yan kungiyar leken asirin Amurka da HKI suna aiki tare wajen ganin sun dakatar da shirin nukiliyan. Daga cikin ayyukan da suke gudanarwa tare da har da aiko da 'virus' zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan na Iran da kuma ci gaba da tattaro bayanai kan masanan na Iran.
Dangane da wannan batu na aiko da kwayoyin cutar kwamfuta irin su Stuxnet da Flame zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan Iran, marubucin ya bayyana cewar: cibiyar leken asirin soji ta HKI da kuma kungiyar leken asirin cikin gida ta Amurka NSI sune suka kirkiro wadannan virus din da nufin lalata kwamfutocin da kuma tattaro bayanan sirri da suke cikinsu.
Ko shakka babu dai Amurka da wani danjuma da danjummai ne a bangaren kulla makirci wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda manufarsu guda ce kamar yadda shugabannin Amurkan suka sha fadi a fili da kuma tabbatar da hakan a aikace. Ko shakka babu irin matsayi da tasirin da Iran take da shi a yankin gabas ta tsakiya, haka nan kuma da yunkurin farkawa ta Musulunci da ke ci gaba da kadawa a duniyar musulmi bugu da kari kan ci gaba da shan kashin da Amurka take fuskanta a gabas ta tsakiyar da kuma raunin da HKI ta yi, dukkanin wadannan abubuwa ne da suka sanya Amurka da kara karfafa irin wannan bakar alaka da ke tsakaninsu don cimma bakaken manufofinsu a kan Iran.
1058024
captcha