Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin asadara na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, Hosni Mubarak tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar yana da hannu kai tsaye wajen killace yankin zirin Gaza domin yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila hidima da kuma kare manufofinta a cikin kasashen larabawa kamar dai yadda aka ka gani a cikin shekarun da ya kwashe yana mulki na zalunci da fir’ananci kan al’ummar Masar.
Wasu rahotanni daga kasar Masar na nuni da cewa wani abu mai fashewa ya tarwatsa bututun da ke isar da iskar gas din kasar zuwa HKI da Jordan a safiyar yau wanda hakan ya kara adadin irin wadannan fashewar zuwa 15 tun daga lokacin da aka kifar da gwamnatin kama-karya ta Hosni Mubarak.
Jami'an tsaron kasar Masar din sun ce fashewar ta faru ne a sanyin safiyar yau din nan lahadi a yankin Al-Tuwail da ke gabashin yankin Sinai inda daga nan ne bututun ya rabu zuwa HKI da kuma kasar Jordan.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewar wadansu mutane dauke da makami ne da suka zo cikin wata mota ne suka tona rami da dasa wadannan abubuwan fashewar a kasar bututun da kuma tayar da su daga nesa. Kamfanin da ke kula da tura iskar gas din dai yace tun da jimawa aka dakatar da tura iskar gas din sakamakon fasa daya daga cikin manyan bututun kamfanin, to sai dai kuma al'ummar yankin sun ce cikin kwanaki ukun da suka gabata kamfanin ya sake dawowa da aikin da ya ke yi na tura iskar gas din lamarin da ake ganin shi ne dalilin kai wannan harin.
Tun da jimawa dai al'ummar Masar suke nuna rashin amincewarsu da alakar cinikin iskar gas da ke tsakanin kasar da HKI wanda gwamnatin Mubarak ta kulla da kuma sayar wa HKIn da iskar gas din kasa da yadda ake sayar da ita a kasuwar duniya.
1058210