Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, gwamnatin kasar Bangadasha ta kirayi mahukuntan kasar Myanmar da su gaggauta mayar da musulmi sama da rabin miliyan da suka kora da sunan cewa sub a ‘yan asalin kasar ba ne tare da bayyana hakan da cewa ya saba wa dukaknin ka’idoji na duniya balantana yan adamtaka da aka yi watsi da ita a cikin wanna aiki na rashin imani da rashin tausayi.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International mai fafutukan kare hakkokin bil'adama ta bayyana cewar jami'an tsaron gwamnatin Myammar da 'yan kabilar Rakhine suna ci gaba da kai hare-hare da take hakkokin al'ummar musulmi kasar ta hanyar yi musu kisan gilla, fyade da cin mutumci.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana cewar jami'an tsaron suna amfani da karfi a kan musulmin da cin mutumcinsu lamarin da ya ke a matsayin take musu hakkokinsu. Har ila yau kungiyar tace jami'an tsaron suna ci gaba da tsare daruruwan musulmin ba tare da an san inda suke ba.
Kisan gillan da ake yi wa musulmin kasar Myammar din dai ya faro ne tun daga watan Mayun da ya gabata inda daga nan ne ya yadu zuwa yankuna daban-daban. Gwamnatin kasar dai tana ganin wadannan musulmin dai a matsayin wadanda ba 'yan kasa ba.
Cibiyoyi da malamai daban-daban na kasashen musulmi ciki kuwa har da nan Iran suna ci gaba da kiran cibiyoyin kasa da kasa da su dau matakan da suka dace wajen kawo karshen wannan kisan kiyashin da ake yi wa musulman Myammar din.
1058220