Bangaren siyasa da zamantakewa, kafofin yada labaran kasar Myanmar sun bayar da rahotannin kisan gillar da ake yi wa musulmi a kasar wanda gwamnati da sauran mahukunta suke da hannu kai tsaye a cikinsa tare da taimakon kasashen ketare da suka yi gum da bakunansu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahabrat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na nahiyar Asia cewa, kafofin yada labaran kasar Myanmar sun bayar da rahotannin kisan gillar da ake yi wa musulmi a kasar wanda gwamnati da sauran mahukunta suke da hannu kai tsaye a cikinsa tare da taimakon kasashen ketare da suka yi gum da bakunansu duk da raya kare hakkin dan adam.
Ambaliyar ruwa ta lashe rayukan mutane akalla 37 a birnin Beijing fadar mulkin kasar China, kafofin watsa labaran cikin gida a kasar China a yau litinin sun bada labarin cewa; Sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai tsanani da aka yi a birnin Beijing na kasar China; hakan ya janyo matsananciyar ambaliyar ruwa da ta lashe rayukan mutane akalla 37, tare bacewar wasu da dama da ba a kai ga tantance yawansu ba, baya ga tilastawa dubban mutane barin gidajensu.
Harkoki sun tsaya cak a birnin na Beijing, kamar yadda aka dakatar da tashin jiragen sama fiye da 500 ko canja lokutan tashinsu, shi dai birnin Beijing na kasar China yana daga cikin shaharrun birane a duniya, kuma mutane kimanin miliyan 20 ne suke rayuwa a cikinsa.
1059178