IQNA

Taro Kan Imam Rida (AS) Karo Na Goma A Taron Baje Kolin Kur’ani

13:23 - July 24, 2012
Lambar Labari: 2376391
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da gudanar da taro baje koli na kur’ani mai tsarki a matsayi na duniya tare da nuna wasu daga cikin sabin kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga a cikin gida da kuma wasu kasashen musulmi da suek da yawan madaba’antu daga cikin kasashen larabawa da na musulmi.
Kmafani dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da taro baje koli na kur’ani mai tsarki a matsayi na duniya tare da nuna wasu daga cikin sabin kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga a cikin gida da kuma wasu kasashen musulmi da suek da yawan madaba’antu daga cikin kasashen larabawa da na musulmi da na yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukaknin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewar ci gaban al'ummar musulmi da wayewarsu sun samo asali ne daga koyarwar alkur'ani da kyawawan dabi'un Musulunci, a jawabin da ya gabatar a gaban taron makaranta da mahaddata da kuma malamai a fannin ilimin alkur'ani mai girma da suka ziyarce shi a yau asabar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewar shaharar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi ya samo asali ne daga dogaronta da Allah karkashin koyarwar alkur'ani mai girma; sannan yayi nuni kan sakamakon da mutum zai samu idan ya dogara da wayewa irin ta kasashen yammaci da ta ginu akan kawar duniya da nisantar kyawawan dabi'u yana mai jaddada cewa; babban misali kan da'awar karya da kasashen yammaci ke yi dangane da kare hakkin bil-Adama shi ne yin shiru kan kisan gillar da ake yi wa dubban musulmai a kasar Myanmar "Bama".
Jagoran ya kuma kara da cewa; wayewar yammaci tun a tsawon daruruwan shekaru da suka gabata har ya zuwa yanzu duk inda suka sanya kafa babu abin da zai bulla sai barna da bautar da dan Adam ta hanyar tatsarsa. Don haka Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fayyace cewar ta hanyar aiki da koyarwar alkur'ani ne kadai za a kai ga samun daukaka, amincin rayuwa, jin dadi na zahiri da badini, kyawawan dabi'u da samun nasara kan makiya addini.
1060758


captcha