Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, mabiya addinin muslunci a kasar Faransa suna gudanar da taruka na addini a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma wanda kuma suna gudanar da su a cikin wannan wata kamar yadda suka saba da hakan ya hada da shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki kop kuma taruka na karatu tare da halarta masu saurare.
A wani labarin kuma dangane hankoron kasashen turai kan masar, jim kadan bayan ganawar da ta gudana tsakaninta da sabon shugaban kasar ta Masar, H. C.ta gudanar da taron amnema labarai tare da takwaranta na kasar Masar Muhammad Amru, inda ta bayyana cewa ganawarta da Muhammad Mursi ta yi armashi matuka, ta ce manufar ziyarar tata dai ita ce nuna cikakken goyon bayan Amurka ga tsarin demokradiyya a kasar Masar, wadda ta kasance sakamako ne na sadukantarwar da al'ummar kasar suka yi.
Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya fadi cewa daga cikin muhimamn abubuwan da take zantawa da jami'an kasar Masar kansu, akwai batun yarjejeniyar zaman lafiya da haramtacciyar kasar Isra'ila, wadda Masar ita ce kasa ta farko a cikin kasashen larabawa da fara rattaba hannu kan irin wannan yarjeneiya tare da gwamnatin yahudawan Sahyuniya a cikin shekara ta 1979, a lokacin mulkin Anwar Sadat, wanda hakan ya fuskanci kakkausar suka daga a'ummar Masar da ma sauran al'ummomin larabawa da na musulmi a duniya, kuma har inda yau take Masar na nan daram kan wannan yarjejeniya.
Amurka dai ta kasance babbar kawa ga Masar a lokacin mulkin hambararren shugaban kasar Masar Husni Mubarak, kuma ita ce kan gaba wajen taimaka masa domin murkushe masu adawa da mulkinsa har tsawon shekaru 32, daga cikin wadanda Husni Mubarak ya gasa musu a hannun kuwa hard a 'yan kungiyar 'yan uwa muuslmi wadda Muhammad Mursi da ta tsayar da Muhammad Mursi takarar shugabancin kasa, lamarin da ya sanya masana kallon ziyarar ta H. Clinton a matsayin wani munafunci na siyasar Amurka.
Ko shakka babu Amurka ita ce kasa ta farko a duniya da ta yi bakin cikin tunbuke Husni Mubarak daga kan kujerar shugabancin kasar Masar, domin kuwa ta rasa wani babban jigo dake kare munufofinta da na haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kasashen larabawa da na musulmi, duk kuwa da cewa Amurka ba ta da aboki na din-din-din amma tana da manufa.
1060609