Kamfanin diallcnin labaran iqna ya ahbarata cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na kamfanin dilalncin labaran kasar Kuwait KUNA, cewa palastinawa sun yi kira ga shugabannin larabawa da su yanke hulda da gwamnatin Myanmar saboda kisan gillar da ta yi wa mabiya addinin muslunci da ke kasar bisa zargin cewa sub a yan asalin kasar ba ne tun shekaru daruruwa da suka gabata ne kakaninsu suka zo kuma ska zauna har suka zama tamkar yan kasa.
Dangane da wannan batu na aiko da kwayoyin cutar kwamfuta irin su Stuxnet da Flame zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan Iran, marubucin ya bayyana cewar: cibiyar leken asirin soji ta HKI da kuma kungiyar leken asirin cikin gida ta Amurka NSI sune suka kirkiro wadannan virus din da nufin lalata kwamfutocin da kuma tattaro bayanan sirri da suke cikinsu.
Ko shakka babu dai Amurka da wani danjuma da danjummai ne a bangaren kulla makirci wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda manufarsu guda ce kamar yadda shugabannin Amurkan suka sha fadi a fili da kuma tabbatar da hakan a aikace. Ko shakka babu irin matsayi da tasirin da Iran take da shi a yankin gabas ta tsakiya, haka nan kuma da yunkurin farkawa ta Musulunci da ke ci gaba da kadawa a duniyar musulmi bugu da kari kan ci gaba da shan kashin da Amurka take fuskanta a gabas ta tsakiyar da kuma raunin da ta yi, dukkanin wadannan abubuwa ne da suka sanya Amurka da kara karfafa irin wannan bakar alaka da ke tsakaninsu don cimma bakaken manufofinsu a kan Iran.
Duk da cewa shugaban Amurkan yana nuna irin kokarin da yake yi wajen ganin HKI ba ta yi gaba gadi wajen kawo wa Iran harin soji ba, to amma kuma duk da hakan yana ci gaba da cewa ba su kawar da wannan batu na kawo hari din ba hakan da nufin kara matsin lamba a kan Iran. To amma a fili yake sannan kuma su kansu Amurkawan sun san cewa Iran ba ta nufin mallakan makaman nukiliya. Babbar manufar dukkanin wadannan abubuwa dai ita ce dakatar da Iran daga irin ci gaba mai ban mamaki da take samu a fagen ilimi da fasaha don haka Amurka da kawayen nata musamman HKI suka dauki wannan siyasa ta kashe masanan nukiliya da kuma barazanar kawo harin soji ko za su cimma wannan manufar.
1060163