IQNA

Lokacin Fadakar Musulmi D aKuma Kawar Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ya Karato

14:01 - July 26, 2012
Lambar Labari: 2377893
Bangaren siyasa da zamantakewa, lokacin fadakar musulmi da kuma gushewar haramtacciyar kasar Isra’ial ya gabato wanda hakan nauyi da ya rataya kan dukaknin al’ummomi na larabawa da na musulmi da su bayar da dukaknin gudunmawarsu wajen tabbbatar da wannan muhimmin lamari.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wakilin kungiyar jihadul islami a jamhuriyar muslunci ya bayyana cewa lokacin fadakar musulmi da kuma gushewar haramtacciyar kasar Isra’ial ya gabato wanda hakan nauyi da ya rataya kan dukaknin al’ummomi na larabawa da na musulmi da su bayar da dukaknin gudunmawarsu wajen tabbbatar da wannan muhimmin lamari kamar dai yadda ya bayyana cewa.
Ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewar gwamnatin Siriya da sojojin kasar suna da karfin murkushe 'yan ta'adda da kansu, a ganawar da ya yi da manema labarai a yau laraba; ministan tsaron kasar Iran Brigadier Janar Ahmad Wahidi ya bayyana cewar gwamnatin Siriya da sojojin kasar suna da karfin kalubalantar duk wani aikin ta'addanci da kansu, kuma a halin yanzu haka suna samun gagarumar nasara a kokarin da suke yi na murkushe 'yan ta'adda a sassa daban daban na kasar.
Wannan furuci na Janar Wahidi ya zo ne a matsayin mai da martaki kan zargin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana taimakawa kasar Siriya ta hanyar karfin soji, har ila yau ministan tsaron kasar ta Iran ya kara da cewar manyan kasashe masu girman kai a duniya suna tattaro kan 'yan ta'adda daga kowane sako na duniya tare da aikewa da su zuwa kasar Siriya, amma suna kokarin kawar da hankula duniya daga kan wannan danye aiki na su ta hanyar zargin kasar Iran da taimakawa kasar Siriya da karfin soji.
1061882


captcha