IQNA

Mahukuntan Saudiyya Sun Dauke Sheikh Namir Daga Kurku Zuwa Riyad

14:01 - July 26, 2012
Lambar Labari: 2377897
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan wahabiyawan Saudiyya sun dauke babban malamin addinin Musulunci na yankin Awamiyya da suke tsare da shi a cikin asibitin soji da ke karkashin tsaro na gidan kurkuku bisa zarginsa da tunzura jama’a su bore zuwa birnin Riyad babban birnin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo rasid cewa, mahukuntan wahabiyawan Saudiyya sun dauke babban malamin addinin Musulunci na yankin Awamiyya da suke tsare da shi a cikin asibitin soji da ke karkashin tsaro na gidan kurkuku bisa zarginsa da tunzura jama’a su bore zuwa birnin Riyad babban birnin kasar ta wahabiyawa.
Ko shakka babu Amurka ita ce kasa ta farko a duniya da ta yi bakin cikin tunbuke Husni Mubarak daga kan kujerar shugabancin kasar Masar, domin kuwa ta rasa wani babban jigo dake kare munufofinta da na haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kasashen larabawa da na musulmi, duk kuwa da cewa Amurka ba ta da aboki na din-din-din amma tana da manufa ta din-din-din.
Wasu masu bin diddigin lamurran da suke faruwa na siyasar kasashen larabawa sun imanin cewa, Muhammad Mursi yana da babban kalu bale a gabansa, kasantuwar cewa da dama daga cikin mutanen da suka jefa masa kuri'a suna da fatan ganin ya yanke alakar kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da taimaka ma al'ummar palastinu, sabanin gwamnatin Husni Mubarak da ta kasance babbar kawa ga Isra'ila, da ake hada baki da ita wajen cutar da al'ummar palastinawa.
Bugu da kari kan hakan, wasu daga cikin kasashen larabawa da suke dasawa da Amurka kuma suke kare manufofinta a cikin kasashen larabawa da na musulmi a halin yanzu kamar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa, ba su lale marhabin da zabar Mursi a matsayin shugaban kasar Masar ba, domin kuwa sun yi iyakacin kokarinsu wajen kasha biliyoyin kudade domin muguda sakamakon zaben na kasar Masar da nufin kayar da Mursi amma hakan bai kai ga nasara ba, wannan ne ma ya sanya Mursi yake kokarin tabbatarwa irin wadannan kasashen larabawa da cewa ba zai mayar da hankali kan abubuwan da suka faru ba, maimakon haka yana neman hadin kansu domin tunkarar gaba.
1062122

captcha