IQNA

Ayatollah Hakim Ya Yi Kakkausar Suka Kan Hare-haren Ta’addancin Da Aka Kai Iraki

19:34 - July 27, 2012
Lambar Labari: 2378437
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addini a kasar Iraki Ayatollah Said Hakim ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da harin ta’addancin da aka kai a sassa na kasar Irakia acikin makon nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari daya akasarinsu fararen hula ne da suka hada da mata da kanan yara.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NUN, cewa daya daga cikin manyan malamin addini a kasar Iraki Ayatollah Said Hakim ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da harin ta’addancin da aka kai a sassa na kasar Irakia acikin makon nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari daya akasarinsu fararen hula ne da suka hada da mata da kanan yara da kuma jamian tsaro.
Da dama daga cikin malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma an ya nakalto daga shafin sadrawa an yanar gizo na Nun cewa, Fathi shazili tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa.
Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu.
1062202
captcha