Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga acikin harshen indiyanci a bangaren da aka baje kayan da suka shafi kur’ani da suka danganci yare na India a matsayin wani mataki na ci gaba da ake samu a wannan bangare domin amfanin masu fahimtar harshen.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga acikin harshen indiyanci a bangaren da aka baje kayan da suka shafi kur’ani da suka danganci yare na India a matsayin wani mataki na ci gaba da ake samu a wannan bangare domin amfanin masu fahimtar harshen wanda daya ne daga cikin muhimman harsuna na kasa da kasa.
Sai kuma bangaren da ke kula da harkoki na ala’du da ilimi a taron baje koli na duniya ya sanar da wani sabon shafin yanar gizo na kur’ani mai tsarki a cikin harshen kasar sin wanda ya kunshi tarjama ta kur’ani da tafsirai da sauran abubuwa da suka danganci kur’ani da aka tarjama a cikin wannan harshe wanda ya zama daya cikin muhimman harsunan duniya.
Duk a wajen taron da an nuna wani littafi mai suna iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka a babban taron baje kolin kur’ani na duniya da ke gudana a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran.
1063527