Bangaren kasa da kasa, daga cikin irin litatfan da aka kawo a wurin taon baje kolin kur’ani mai tsarki na duniya har da lttafi kan rayuwar mashhurin malamin nan na kasar Masar Mustafa Isma’il wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada karatun kur’ani mai tsarki a ckin duniya musulmi tare da samar da dalibai da suka zama taurari a wannan bangare.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa, cewa daga cikin irin litatfan da aka kawo a wurin taon baje kolin kur’ani mai tsarki na duniya har da lttafi kan rayuwar mashhurin malamin nan na kasar Masar Mustafa Isma’il wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada karatun kur’ani mai tsarki a ckin duniya musulmi tare da samar da dalibai da suka zama taurari a wannan bangare, a cikin kasar ta Masar da kuma sauran kasashen larabawa.
A wani labarin kuma na daban shugaban kasar Masar Muhammad Mursi zai kawo ziyarar aiki a nan kasar Iran a watan Agusta domin halartar taron koli na kungiyar Yan Ba Ruwanmu wanda za a gudanar a birnin Tehran hakazalika zai tattauna batutuwa da su ka shafi kasashen biyu, tare da jamian gwmantain kasar Iran, jaridar Al-Safir ta kasar Labanan ce ta kawo wannan labari tare da kuma cewa ana tsammanin za a sami kyautatuwar alaka tsakanin Iran da Masar a yan makonni masu zuwa.
Tun bayan faduwar gwamnatin Husni Mubarak na kasar Masar jamian gwamanatin Iran da na Masar suke ta bayyana shawaarsu ta maida cikakken huldar jakadanci tsakanin kasashen nasu, minsitan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salehi ya gana da tsohon tawaran aikinsa na kasar Masar Nabil al-Arabi a gefen zauren taron kungiyar Yan Ba Ruwanmu da aka yi a garin Bali na kasar Indonisiya, inda kuma suka yi musayar raayi kan hanyoyin karfafa alakoki tsakanin Tehran da Alkahira.
1063610