IQNA

Ana Guadanar Da Zanga-Zangar Nuna Goyon Bayan Ga Al'ummar Myanmar

11:16 - July 29, 2012
Lambar Labari: 2379714
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutane sun gudanar da wata gagarmar zamga-zanga a kasar Jamus domin nuna goyon baya ga al'ummar kasar Myanmar da ake yi wa yankan rago ba kakkautawa kamar yadda aka gudanar da wannan gangamin a wasu branan baya ga birnin Berlin.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazira cewa, daruruwan mutane sun gudanar da wata gagarmar zamga-zanga a kasar Jamus domin nuna goyon baya ga al'ummar kasar Myanmar da ake yi wa yankan rago ba kakkautawa kamar yadda aka gudanar da wannan gangamin a wasu branan baya ga birnin Berlin fadar mulkin kasar ta Jamus.

Bayanin ya ci gaba da cewa a nasu bangaren mutanen yankin Kashmir karkashin ikon kasar India sun dakatar da harkokin kasuwanci da kuma ayyukansu don nuna fushinsu da yadda sojojin kasar ta India suka kashe wani mutum a ranar tarlatan da ta gabata.

Yasin malik shugaban kungiyar “Jamu anda Kashmir Libration Front” ya fadawa gidan television na Presstv cewa, sojojin kasar India sun kashe Hilal Ahmad Dar dan shekara 20 a duniya ne bayan ya fito daga masallaci ne a daren tarlatan da ta gabata, kuma baya dauke da makami.

Amma jami’an tsaron kasar India sun bayyana cewa mutumin yana daga cikin tsagren yankin Kashmir wadanda suke dauke da makamai, gamayyan jam’iyyun siyasar yankin Kashmir wato “hurriyar conference” ne suka kira yajin aikin na jiya asabar wanda ya dakatar da dukkan zirga zirga da kuma harkoki a yankin na Kashmir. Shugaban gungun jam’iyyun siyasar Sayyeed Ali Sha Gilani ya bayyan cewa sojojin sun kashe Hilal ne ba tare da yana dauke da makami ba. Don haka sun yi Allah wadai da wannan kissan.

Ministan tsaron kasar India A.K. Anthony tare da wasu jami’an gwamnatin kasar sun kai ziyara zuwa yankin a jiya asabar kuma ya bayyana cewa za’a gudanar da bincike don tabbatar da zargin da mutanen yankin sukewa jami’an tsaron kasar.

1064250




captcha