Bangaren kasa da kasa, cibiyoyin ilimi na Hausa da ke birnin Karbala mai alfarma sun yi kira da adauki kwararn matakai na kare wurare masu tsarki da suke cikin kasar daga harin yan ta’adda da suke kokarin ganin sun mayar da kasar wani wuri na tashin hankali tare da haramta wa masu ziyara zuwa wuraren addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa cibiyoyin ilimi na Hausa da ke birnin Karbala mai alfarma sun yi kira da adauki kwararn matakai na kare wurare masu tsarki da suke cikin kasar daga harin yan ta’adda da suke kokarin ganin sun mayar da kasar wani wuri na tashin hankali tare da haramta wa masu ziyara zuwa wuraren addini da suke cikin kasar.
Gwamnatin kasar Rahsa ta bayyana cewa bazata kyale kasashen tarayyar turai su binciki jiragen ruwa wadanda suke dauke da tutar kasar Rasha zuwa kasar Syria ba, karkashin sabon takunkumin da suka dorawa kasar. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ne ya bayyana haka a jiya Asabar kuma ya kara da cewa kasar Rasha ba zata mutunta takunkumin da kasashen na turai suka dorawa kasar ta Syria ba. Don a fadinsa, takunkumin ya na nan a matsayin kofar rago ga kasar Syria ta sama da kasa ne.
Kasashen Turai da Amurka da kuma wasu kawayensu na sauran kasashen musulmi suna bada tallafin makamai da kayakin sadarwa ga yan tawayen kasar Syria, da nufin kifar da gwamnatin Bashar Al-asad. A halin yanzu dai sojojin kasar Syria suna ci gaba da fafatawa da yantawayen a yankunan da daman a kasar. A cikin makonnin da suka gabata ma, yan tawayen tare da taimakon kasahen na yamma sun tada wani bom wanda ya kashe manya manyan jami’an tsaron kasar ta Syria. Wadanda suka hada har da ministan tsaron kasar da mataimakinsa.
1064694