IQNA

An Nuna Kwafin Kur’ani Mai karanta Da Aka Rubuta Ruwan Azurfa

17:48 - July 29, 2012
Lambar Labari: 2380174
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki mafi karanta da aka rubuta da ruwan azurfa a kan takardu wanda hakan zai zama babban aiki na musamman da za a nuna a matsayin babban ci gaban ta bangaren kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Muslim Times cewa an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki mafi karanta da aka rubuta da ruwan azurfa a kan takardu wanda hakan zai zama babban aiki na musamman da za a nuna a matsayin babban ci gaban ta bangaren kur’ani mai tsarki a cikin duniyar musulmi.
Wannan batu na uku da muka ambata, wato yin aiki na hankali da adalci shi ne muhimmin dalilin da ya taimaka wa masu juyi wajen samun gagarumar nasara a baya bayan a kasashe kamar Tunisiya da Masar. A fili yake cewa tsattsaurar raayi yana kawo rarraba a cikin alumma, da bata fuskar Musulunci ta hakika, da kuma ba da dama ga kasashe majiya karfi masu kuma adawa da Musulunci su yi katsalanda a kasashen Musulmi. Wani muhimmin abu kuma shi ne rawar da matasa suka taka a farkawar alummomin Musulmi a tsawon shekara daya da ta gabata, kuma wannan guguwa ta girgiza masu iko kama daga arewacin Afirka har zuwa kasashen yankin Tekun Pasha.Wannnan guguwa ta kawar da shugabanni yan kama karya wadanda kuma iyayen gidansu Turawa suke kira masu daidaiton siyasa.
Wato Zainulabidin bin Ali na Tunisiya, Husni Mubarak na Masar da Ali Abdallah Saleh na Yaman, wadanda kuma yan koren kasashen Yamma ne. Ko shakka ba bu matasa na kowace alumma babban rukuni ne wanda kuma ginshiki ne daga cikin ginshikan da kasa zata dogara a kansu wajen kawo sauyi da kuma tabbatar da shi. Ita ma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma nasarar juyin juya halinta da kuma ci gaba da wanzuwarsa net a hanyar aiki da matasa a kowane fage kuma da haka ne kasar Iran din ta ketare dukkan tarkon da manyan kasashe makiya suka kulla mata kuma har a kullum suke kulla mata.
1064214






captcha