Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na nayanr gizo cewa, masana da dama suna ganin cewa kasashen yammacin turai sun kasa cimma burinsu na kawar da gwamnatin Syria kamar yadda suka yi a kasar Libya wanda hakan ya kawo aksrejhn mulkin marigayi kanar Gaddafi a cikin shekarar da ta gabata ta hanyar yi masa kisan gilla a garinsa na haihuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun bayan harin da aka kai kan babban ginin majalisar tsaron kasa a birnin Damascus na kasar Syria a ranar Laraba da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ministan tsaron kasar da mataimakinsa, dakarun gwamnatin kasar ta Syria suka lashi takobin shiga kafar wando daya da 'yan ta'adda da suke kaddamar da irin wadannan hare-hare a cikin kasar, wadanda suke samun goyon baya da taimakon Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da sauran kasashen turai, gami da 'yan koransu daga cikin gwamnatocin larabawa.
A cikin wani bayani da rundunar sojin Syria ta fitar 'yan sa'oin da suka gabata, ta tabbatar da cewa nan da sa'oi 24 zuwa 48 za a kammala murkushe 'yan ta'adda da suka sadado cikin birnin Damascus suna harbe-harbe, tare da korar mutane daga wasu unguwanni da ke cikin birnin, a daren jiya kawai sojojin gwamnatin Syria sun kashe 'yan ta'adda sama da 150 da suke dauke da makamai a cikin birnin Damascus da wasu yankuna na kasar, yayin da wasu daruruwa suka ajiye makamansu tare da mika wuya bayan da sojojin na Syria suka yi musu kofar raggo. Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin gawawwakin 'yan ta'addan da aka samu wadanda sojin gwamnatin Syria suka harbe bayan musayar wuta mai tsanani a yankin Maidan da Qabun a cikin sa''oi da suka gabata, akwai 'yan kasashe daban-daan da suka hada da Libya, Tunisia, Saudiyya, Kuwait Pakistan Lebanon da sauransu, lamarin da ya sanya da dama daga cikin masu bin diddigin lamuran da ke faruwa a Syria suke ganin cewa, abin da ke faruwa a kasar dadadden shiri ne da aka shirya daga wajen kasar, da ba shi da wata dangantaka da boren kasashen larabawa, domin kuwa Amurka da sauran kasashen turai da yan koransu daga cikin kasashen larabawa su ne suke jagorantar rikicin da ke faruwa a Syria, su ne suke aikewa da mayaka da makamai da kudade, wani ban mamaki kuma a nan shi ne, daga cikin mayakan da Amurka da sauran kasashen larabawa suke aikewa zuwa Syria har da 'yan alkaida, wadanda Amurka da turawa suka ce suna yaki da su a Iraki da kuma Afghanistan da Pakistan.
Masana kan harkokin soji sun yi imanin cewa, ko shakka babu yanayin yadda aka kai hari kan babban ginin majalisar tsaron kasar Syria a ranar Laraba da ta gabata, da kuma irin bama-baman da aka yi amfani das u wajen kai harin, na tabbatar da cewa akwai hannun wasu manyan kasashen duniya, kuma manufar hakan ita ce karya zuciyar sojojin kasar domin su balle, to amma sai tsafi ya juya kan boka, domin kuwa hakan ya zaburar da sojojin kasar fiye da kowane lokaci tun da aka kunna wutar rikicin, wajen ganin cewa sun kawo karshen 'yan ta'adda a kasar, bababn dalili kan hakan kuwa shi ne yadda su kansu kasashen turai da suke daukar nauyin 'yan ta'addan suka yarda cewa yaran nasu kam a halin yanzu suna yaba wa aya zaki a hannun dakaron Syria, dalili na biyu kuma shi ne yadda a jiya Lahadi 'yan ta'adda na Syria suka yi kira ga dakarun gwamnati da a dakatar da bude wuta na wani dan lokaci, kiran da rundunar sojin ta yi watsi da shi.
1064182