IQNA

Babbar Cibiyar Qods Ta Gargadi Kan Bazuwar Mamayar Yankunan Birnin Mai Alfarm

12:50 - July 30, 2012
Lambar Labari: 2380855
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar da ke kula da harkoki kan birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma da ta hada wakilai daga kasashen duniya musamman na musulmi da na larabawa ta yi gargadi dangane da yunkurin da haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da yin a ganin cewa ta mamaye dukkanin yankunan birnin.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine Info, cewa babbar cibiyar da ke kula da harkoki kan birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma da ta hada wakilai daga kasashen duniya musamman na musulmi da na larabawa ta yi gargadi dangane da yunkurin da haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da yin a ganin cewa ta mamaye dukkanin yankunan birnin mai alfarma da ke yahudawa suke cin karensu abbau babbaka acikinsa.
Majiyar asibiti ta tabbatar da cewa a safiyar yau litinin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kashe wani Bapalastine guda da kuma raunana wasu guda biyu sakamakon bude wuta da suka yi wa motarsu a wani wajen bincike da ke yammacin kogin Jordan.

Majiyar asibitin Palastinu ta bayyana cewar shi dai wannan mutumin dan kimanin shekaru 40 da sauran Palastinawan da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka raunana suna tafiya ne a kan hanyarsu ta zuwa Qudus don yin salla.

Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suke aikata irin wannan danyen aikin na bude wuta kan motocin Palastinawan ba, lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar wasu daga cikinsu da kuma raunana wasu.

1064987







captcha