Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na walfajr cewa, a cikin wannan makon an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta yankin Katif da ke gabacin kasar saudiyya wanda akasarin mazauna yankin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka ne da suke fusknatar zalun da danniya daga mahukunta wahabiyawa.
A wani labarin kuma na daban Sojojin Siriya sun sami nasarar kwato yankin Salahudden na garin Halab mai matukar muhimmanci daga hannun 'yan tawaye masu dauke da makami na kasar sannan kuma sojojin suna ci gaba da kokarin fatattakansu daga sauran yankuna na garin.
Rahotannin da suke fitowa daga garin Halab din suna nuni da cewa sakamakon hare-haren da sojojin Siriyan suka kaddamar cikin kwanaki biyun da suka gabata sun sami nasarar 'yanto yankuna daban-daban na birnin. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo daya daga cikin jagororin sojojin Siriya a Halab yana cewa cikin 'yan kwanaki masu zuwa za su sami damar tsarkake garin daga 'yan ta'addan da suka yi masa kawanya wadanda kuma suke samun makamai daga kasashen Turkiyya da Saudiyya da Qatar. Jami'in sojan yace daya daga cikin dalilan da suke kawo cikas wajen gamawa da 'yan ta'addan shi ne kokarin da sojojin suke yi wajen kiyaye lafiyar fararen hula da 'yan ta'addan suke garkuwa da su a wasu lokuta. Wasu rahotannin kuma sun tabbatar da cewa sojojin Siriyan sun sami nasarar kashe wani adadi mai yawan na 'yan ta'addan da kama wasu daga cikinsu bugu da karin gano ma'ajiyan makamai daban-daban da 'yan ta'addan suke amfani da su.
A wata sabuwa kuma wasu rahotanni suna nuni da hannun kasashen Jordan, Saudiyya da Turkiyya ciki harin da aka kai ofishin cibiyar tsaron kasar Siriya a kwanakin baya da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan jami'an tsaron kasar su hudu ciki kuwa har da ministan taro da mataimakinsa.
Kamfanin dillancin labaran Siriya online ya jiyo wata majiyar hukumar leken asirin kasar Rasha wacce take gudanar da bincike da musabbabin harin tana cewa an gano wasu bayanai da suke nuni da hannun kungiyoyin leken asirin Saudiyya, Jordan da Turkiya cikin wannan danyen aikin.
1065002