IQNA

Masu Kishin Isalam A Jordan Sun Yi Allawadai da Harin Yahudawa A Qods

10:48 - July 31, 2012
Lambar Labari: 2381666
Bangaren kasa da kasa, masu kishin islama a kasar Jordan kakkausar suka da yin Allawadai da matakan da yahudawan sahyuniya suke dauka na wuce gonad a iri wajen kisan gilla kan fararen hula palastiwa a birnin Qods da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI, cewa masu kishin islama a kasar Jordan kakkausar suka da yin Allawadai da matakan da yahudawan sahyuniya suke dauka na wuce gonad a iri wajen kisan gilla kan fararen hula palastiwa a birnin Qods da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da ke birnin mai alfarma.

A wata tattaunawa da ya yi da tashar CBS din, Dan Raviv ya bayyana cewar a cikin kungiyar leken asirin HKI akwai wani bangare da aka ware da aka ba su aikin kashe masanan nukiliyan Iran. Har ila yau a cikin wannan littafin, marubucin ya yi ishara da wasu daga cikin ayyukan ta'addanci da kisan gilla da kungiyar din ta aikata a biranen Beirut da Damaskus na kasashen Labanon da Siriya inda yake cewa a halin yanzu 'yan kungiyar leken asirin Amurka da HKI suna aiki tare wajen ganin sun dakatar da shirin nukiliyan. Daga cikin ayyukan da suke gudanarwa tare da har da aiko da 'virus' zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan na Iran da kuma ci gaba da tattaro bayanai kan masanan na Iran.

Dangane da wannan batu na aiko da kwayoyin cutar kwamfuta irin su Stuxnet da Flame zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan Iran, marubucin ya bayyana cewar: cibiyar leken asirin soji ta HKI da kuma kungiyar leken asirin cikin gida ta Amurka NSI sune suka kirkiro wadannan virus din da nufin lalata kwamfutocin da kuma tattaro bayanan sirri da suke cikinsu. Ko shakka babu dai Amurka da HKI wani danjuma da danjummai ne a bangaren kulla makirci wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda manufarsu guda ce kamar yadda shugabannin Amurkan suka sha fadi a fili da kuma tabbatar da hakan a aikace. Ko shakka babu irin matsayi da tasirin da Iran take da shi a yankin gabas ta tsakiya, haka nan kuma da yunkurin farkawa ta Musulunci da ke ci gaba da kadawa a duniyar musulmi bugu da kari kan ci gaba da shan kashin da Amurka take fuskanta a gabas ta tsakiyar da kuma raunin da HKI ta yi, dukkanin wadannan abubuwa ne da suka sanya Amurka da HKI kara karfafa irin wannan bakar alaka da ke tsakaninsu don cimma bakaken manufofinsu a kan Iran.

Duk da cewa shugaban Amurkan yana nuna irin kokarin da yake yi wajen ganin HKI ba ta yi gaba gadi wajen kawo wa Iran harin soji ba, to amma kuma duk da hakan yana ci gaba da cewa ba su kawar da wannan batu na kawo hari din ba hakan da nufin kara matsin lamba a kan Iran. To amma a fili yake sannan kuma su kansu Amurkawan sun san cewa Iran ba ta nufin mallakan makaman nukiliya. Babbar manufar dukkanin wadannan abubuwa dai ita ce dakatar da Iran daga irin ci gaba mai ban mamaki da take samu a fagen ilimi da fasaha don haka Amurka da kawayen nata musamman HKI suka dauki wannan siyasa ta kashe masanan nukiliya da kuma barazanar kawo harin soji ko za su cimma wannan manufar.

1066151


captcha