IQNA

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Hana Gudanar Da Buda Baki A Qods

11:35 - July 31, 2012
Lambar Labari: 2381780
Bangaren kasa da kasa, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana daruruwan palastinawa gudanar da buda baki a cikin masallacin Qods mai alfarma kamar yadda suka saba gudanarwa a kowace shekara a wani mataki na tsananta zaluncinsu kan al'ummar palastinu mazauna wannan birnin mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Egypt Independent, cewa sojojin yahudawan sahyuniya na haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana daruruwan palastinawa gudanar da buda baki a cikin masallacin Qods mai alfarma kamar yadda suka saba gudanarwa a kowace shekara a wani mataki na tsananta zaluncinsu kan al'ummar palastinu mazauna wannan birnin mai alfarma da Allah ya ambace a cikin kur'ani mai tsarki.

Wannan dai bas hi ne karon farko da sojojin yahudawan ahyuniya suke hana palastinawa shiga masallacin ba domin gudanar da harkokinsu an ibada, domin kuwa tun amakon day a gabata an hana su shiga domin su yi salla, kuma hakan bay a rasa nasaba da gabatowar lokacin gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga masallacin Qods mai alfarma da marigayi Imam Khomeini ya asssa tun tsawon shekaru kusan talatin da suka gabata.

Rahotannin sun tabbatar da cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana daruruwan palastinawa gudanar da buda baki a cikin masallacin Qods mai alfarma kamar yadda suka saba gudanarwa a kowace shekara a wani mataki na tsananta zaluncinsu kan al'ummar palastinu mazauna wannan birnin mai alfarma, da kuma wurare masu tsarki da ke cikinsa.

1066045




captcha