IQNA

Mutanen Kasar Libya Sun Bukaci A Nuna Goyon Baya Ga Musulmin Myanmar

9:30 - August 01, 2012
Lambar Labari: 2382654
Bangaren kasa da kasa, mutanen kasar Libya sun bukaci da a dauki tsauraran matakai n atakurwa da matsin lamaba kan mahukuntan kasar Myanmar dangane da kisan gillar da suke yi kan mabiya addinin musulunci na kasar da sunan wai bay an asalin kasar ba ne duk kuwa da cewa kakaninsu sun share tsawon daruruwan shekaru da zuwa kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Libya yaum, cewa mutanen kasar Libya sun bukaci da a dauki tsauraran matakai n atakurwa da matsin lamaba kan mahukuntan kasar Myanmar dangane da kisan gillar da suke yi kan mabiya addinin musulunci na kasar da sunan wai bay an asalin kasar ba ne duk kuwa da cewa kakaninsu sun share tsawon daruruwan shekaru da zuwa kasar wadda ke fama da matsanancin talauci.

A wani labara dangane da siyasar kasar ta Libya kuwa, Hukumomin rikon kwaryar kasar sun ce a ranar 8 ga watan Agusta mai kamawa ne za su danka ragamar mulkin kasar a hannun sabuwar Majalisar Dokokin da aka zaba a ranar 7 gawatan Yulin da gabata. Wani mai magana da yawun Majalisar rikon kwaryar mai suna Othman Ben Sassi, ya ce tuni aka cimma matsaya kan wannan batu tsakaninsu da sabuwar Majalisar da al'ummar kasar ta zaba domin tafiyar da al'amurran kasa da kuma rubuta wa kasar sabon kundin tsarin mulki da kuma shirya zabukan gama gari a nan gaba.

Sabuwar Majalisar dai tana da kujeru 200, 80 daga cikinsu an ware su ne domin jam'iyyun siyasa, yayin da sauran kujerun aka bar wa 'yan takara masu zaman kansu, kuma kamar yadda sakamakon zaben ya nuna, kawancen sabbin jam'iyyun siyasa guda 40 da ba su da alaka da addini ne suka samu kujeru 39, yayin da masu ra'ayin Islma suka samu kujeru goma sha bakwai.

1067246
captcha