Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iba, cewa al’ummar kasar Bahrain na ci gaba da gudanar da gangami a dukkanin yankunan kasar domin tabbatarwa mahukuntan cewa suna kan bakansu na neman hakkokinsu ba tare da wani sassauci ko saryar da hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu a ‘yan kasa ba wanda kuma abin da suke yi bai hannun riga da dokoki na kasa da kasa ba.
A wani labarin kuma dangane da kasar Sudan hukomomin kasar sun bayar da umurnin rufe dukkanin makarantu da ke birnin Nyala wanda shi ne babban birni a yankin Darfur ta Kudu inda a jiya aka gudanar da tarzoma tare da haddasa asarar rayukan mutane akalla 8. Wani gidan rediyo da ke garin na Nyala ya sanar a sanyin safiyar yau cewa gwamnati ce ta bayar da umurnin rufe makarantun domin hana ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Umar Hasan Albashir kamar dai yadda aka yi a jiya, kuma yanzu haka an barbaza dimbin jami'an tsaro a kan titunan birnin.
Tun dai a ranar 16 ga watan yunin da ya gabata ne aka soma gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a birane da dama na kasar ta Sudan, wannan kuwa bayan da gwamnati ta sanar da shirinta na tsuke bakin aljihu sakamakon matsalolin tattalin arziki da kasar ta fada.
1067173