Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na jaridar riyad da ake bugawa a kasar Sudiyya, cewa kungiyar kasashen musulmi tana gudanar da zama domin tatatuna batun kasar Maynamar da kuma halin da musulmin kasar suke ciki tare da sanin hanyuyin da za a bi wajen kara matsa lamba kan mahukuntan kasar da su dakatar da kisan musulmi, ko kuma a dauki mataki na bai daya akan kasar.
musulmin kasar Mayammar sun zama karen gwajin dafi na nuna kin jiki da tsangwana. Mabiya addinin Budda masu tsattsauran ra'ayi a yankin Rakhtin da ke yammacin kasar suna yi wa musulmin kisan gilla saboda kawai su musulmi ne. Ita kuwa gwamnatin kasar ta sanya ido tana kallon abinda ya ke faruwa ba tare da dauki matakin da ya dace ba. Har ila yau, kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama a duniya sun yi gum da bakunansu kai kace wadanda ake kashewa ba bil'adama ba ne da su ke riya cewa suna karewa hakki. Kawo ya zuwa yanzu lamirin duniya bai girgiza ba akan kisan da ake yi wa musulmin mayyamar da kona gidajensu da shagunansu na kasuwanci. Babu wanda ya zubar da koda hawaye akan musulmi dubu dari takwas da rayuwarsu ta ke fuskantar bakar wahala.
Shin saboda mutanen da ake kashewa a muyammar musulmi ne, ko kuma saboda tsiraru ne? Yadda al'amurra su ke tafiya a cikin kasar ta Muyammar a yanzu na nuni da cewa za a ci gaba da samun asarar rayuka anan gaba, tunda dai babu alamar za a takawa masu makasa birki. Ga dukkanin alamu'kisan da 'yan budda su ke yi wa musulmi a cikin Muyammar suna yi ne da tallafin gwamnatin kasar. Su ke kuma korarsu daga gidajensu da maida su zama 'yan gudun hijira na tilas. A tsammani shi ne addinin Budda wanda ya yi imani da halin kirki da kyautatawa halittu, da s u ke kira Neravana, su zama masu kyautatawa abokan zama da su.
A lokacin da 'yan taliban su ka tarwatsa gumakan Budda a Afgahnistan , wadannan musulmin da ake kashe wa a yanzu sun yi Allah wadai da Taliban su ka kuma bayyana abinda su ka yi da cewa keta ce da mugunta. Daruruwan shekaru musulmin kasar Thalidan su ka yi suna rayuwa da mabiya addinin Budda, amma ana samun sauyin siyaya a cikin kasar sai abokan zamansu su ka ci amanarsu da fara kashe su.
1067000