IQNA

Batun Kafa Gwamnatin Rikon Kwarya Ta Yan Adawar Syria Dalili Ne Na Rarrabarsu

23:06 - August 02, 2012
Lambar Labari: 2383849
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da wasu daga cikin yan adawar Syria da suke zane a kasashen ketare suna samun taimako daga kasashen turai suke kokarin kafa wata gwamnati ta rikon kwarya wasu daga cikinsu na ganin cewa yin hakan zai kara tabbatar ma duniya cewa akwai babbar baraka a tsakaninsu kamar yadda hakinin lamarin yake.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa a daidai lokacin da wasu daga cikin yan adawar Syria da suke zane a kasashen ketare suna samun taimako daga kasashen turai suke kokarin kafa wata gwamnati ta rikon kwarya wasu daga cikinsu na ganin cewa yin hakan zai kara tabbatar ma duniya cewa akwai babbar baraka a tsakaninsu kamar yadda hakinin lamarin yake, wanda kuma kuma safke shugaban majalisar yan tawayen dama ya tabbatar da hakan.
A bangare guda kuma shugaba Barak Obama na kasar Amurka ya bada umurni a asirce ga hukumomin tsaron kasar daban daban, kamar CIA na su tallafawa yan tawayen kasar Syria don ganin bayan gwamnatin shugaba Bashar Al-asad. Gwamnatin kasar Amurka ta dau wannan matakin ne bayan da, ita da kawayenta suka kasa samar da kuduri na kara takurawa gwamnatin kasar Syria a komitin tsaro na MDD a watan da ya gabata.
Amma a lokacinda yan jaridu suka tuntubi kakakin fadar ta white House Tommy Vietor ya ki ya ce uffan kan maganar. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya tabbatar da cewa kasashen Saudia da kuma Qatar sun samar da wani sansanin horar da yan tawayen na kasar Syria a garin Adana, na kasar Turkiya mel 60 daga kan iyakar kasar Syria.
Har’ila yau kasar Amurka tana da sansanin sojojinta da kuma dimbin jami’an tsaronta a garin. A jiya laraba ma gwamnatin kasar ta Amurka ta bada sanarwan kebe dalar Amurka miliyon 25 don tallafawa yan tawayen a bangaren da bai shafia makamai ba. Haka nan masu arziki a kasashen Qatar da Saudia suna bada tallafi kudade masu yawa ga yan tawayen.
1068441

captcha