Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa Abdlmalik Husi joran mabiya Husi a yanin arewcin kasar Yeman ya bayyana cewa babban makiyin al’ummar musulmi a halin yanzu haramtacciyar kasar Isra’ila ce kuma ita ce hankoron ganin ta juya yunkurin da mutanre suke yi a cikin kasashen larabawa na neman samar da sauyi na adalci, zuwa ga manufarta da kuma yadda suke fatan ganin larabawa sun da gwamnatocinsu sun koma karkashinsu baki daya.
Gwagwarmayar musulunci ta koyar da haramtacciyar kasar Isra’ila babban darasi wanda ba za ta tabata manta da shi ba a cikin tarihinta kuma hakan ya sanya yahudawan sahyuniya sake tunani kan cewa za a iya lallasa su a hannun kungiyoyin gwagwarmaya masu tsarkakakkiyar zuciya.
Ko shakka babu a wannan zamani gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta hizbulla ta fitar da wani bayani da acikinsa take mayar da martani kan furucin sakataren majalisar dinkin duniya dangane da makaman kungiyar, inda bayanin ya ce hakkin lebanon ta mallaki makamai na gwagwarmaya domin mayar da martani kan wuce gonda irin yahudawan sahyuniya kan al’ummar Lebanon.
A cikin bayanin kungiyar ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira rashin lamiri na mutumin da ake kira sakataren majalisar dinikin duniya, wanda ya kamata ya kare hakkokin mutane na kasashen duniya, amma maimakon hakan sai mayar da hankali wajen kare barnar da yahudawan sahyuniya suke aikatawa, tare da ba su kariya ta hanyar yin amfani da kujerarsa.
A lokutan baya ne Ban ki moon ya bayyan acewa, makaman da kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hzibullah take mallaka barazana ce ga ita kanta kasar Lebanon.
1068493