Bangaren kasa da kasa, a cikin wannan makon za a gudanar da zaman taro kan kisan kiyashin da aka yi mabiya addinin musulunci a kasar Myanmar babu gaira babu sabar tare da sanin matakan da ya kamata a dauka kan wannan lamari a bisa dokoki da suka shafi hakan ada kasashen duniya sukla rattaba hannu a kansu.
Kamfanin dillanin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa a cikin wannan makon za a gudanar da zaman taro kan kisan kiyashin da aka yi mabiya addinin musulunci a kasar Myanmar babu gaira babu sabar tare da sanin matakan da ya kamata a dauka kan wannan lamari a bisa dokoki da suka shafi hakan ada kasashen duniya sukla rattaba hannu a kansu, domin hukunta duk wani mai hannu cikin lamarin.
jamhuriyar musulunci ta Iran ta jaddada wajabcin girmama sauran addinai na duniya da mabiyansu a duk inda suke domin kuwa hakan shi ne babban abin da zai kawo zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin duniya baki daya tare da kauce wa duk wani yunkuri na makiyan al’ummomin duniya da suke son ganin rashin fahimta ya kara yawa a tsakaninsu.
Baynain ya ce za a gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar Birtaniya tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar da ma wasu kasashen ketare.
Wannan zaman taro yana daya daga cikin muhimamn taruka da kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu na muslunci ke shirin shiryawa abirnin na London, kuma ya samu karbuwa daga mutane da dama da aka aike musu da goron gayyatar halartar taron, musamman ma masana da malaman addinin muslunci na kasar da kuma wasu kasashen musulmi da na larabawa.
1068692