IQNA

Saboda Yawan Yarukan Da Iqna Ke Da Su Sun Samu Wurare Masu Yawa A Baje Kolin Kur’ani

15:11 - August 03, 2012
Lambar Labari: 2384140
Bangaren kasa da kasa, kasantuwar kamfanin dilalncin labaran kur’ani mai tsarki na jamhuriyar musulunci ta Iran yana da yaruka da dama yake watsa labaransa ta hanyarsu wannan ne ya sanya suka samu wurare masu yawa a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ke gudana ahalin yanzu.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa n cikin gida cewa, malam Muhammadi Iraki ya bayyana cewa kasantuwar kamfanin dilalncin labaran kur’ani mai tsarki na jamhuriyar musulunci ta Iran yana da yaruka da dama yake watsa labaransa ta hanyarsu wannan ne ya sanya suka samu wurare masu yawa a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ke gudana a halin yanzu a wurin da aka saba gudanar da wannan babban taro na baje kolin kur’ani.
Hojjatol Muhammadi Islam Iraki daya daga cikin mambobin majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci a jamhuriyar muslunci ta Iran ya kai wata zirar rangadi ne a taron baje koli na kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa yanzu a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran, wanda shi ne na ashirin da ake gudanar da shi tare da halartar wakilan cibiyoyin addini na ciki da waje.
Jamhuriyar mulsunci ta Iran dai tana baiwa lamarin kur’ani matukar muhimamnci kasantuwarsa shi ne asasia cikin addini da ke yin haanunka mai sanda ga musulmi zuwa ga bin sahihin tafarkin da Allah ya umurci manzonnsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da ya bi, kuma kur’ani shi ne abokin hadin manzon Allah, kamar yadda ya zama abokin hadin limaman gidansa tsarkaka abayansa.
1068883






















captcha