IQNA

An Rarrab Kwafin Kur’ani Mai Tsarki Da Akabuga Da Kure A Masallatan Algeria

15:10 - August 03, 2012
Lambar Labari: 2384148
Bangaren kasa da kasa, an raba kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga da kure a kasar Algeria wanda ma’aikatar kula da ahrkokin addini ta kasar ta dauki nauyin bugawa da kuma rabawa a masallatai a cikin wannan wata mai alfarma na ramadan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Shoroyq online, cewa an raba kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga da kure a kasar Algeria wanda ma’aikatar kula da ahrkokin addini ta kasar ta dauki nauyin bugawa da kuma rabawa a masallatai a cikin wannan wata mai alfarma na ramadan.
Ma’aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta dauki wannan matakin ne domin karawa yawan kur’anai da mutane mutane suke amfani da su a cikin watan ramadan, amma kuma daga bisani daya daga cikin limaman masallatai ya gano cewa babu wasu daga cikin suririn kur’ani, yayin da aka canja wuraren wasu ayoyi, a kan malamin ya kirayi ma’aikatar da ta dauki matakan gagagwa wajen tattara wadanan kwafi-kwafi na kur’ani daga hannun mutane.
Rahoton ya kara da cewa an raba kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga da kure a kasar Algeria wanda ma’aikatar kula da ahrkokin addini ta kasar ta dauki nauyin bugawa da kuma rabawa a masallatai a cikin wannan wata mai alfarma na ramadan da musulmi suke yin azumi a cikinsa.
1068399


captcha