IQNA

An Nuna Samfuri Na Tafsirin Kur’ani Mai Tsarki Da Aka Tarjama A Cikin harshen Spananci

17:48 - August 04, 2012
Lambar Labari: 2385249
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani samfurin kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen spananci daga cikin manyan ayyukan da babba mamalimn addinin mulunci Ayatollah Shirazi ya gudanar wanda kuma ake lissafa shi a cikin manyan tafsirai na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbaba agare shi a da iylan gidansa.
Kamfanin dilalnci9n labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na cikin gida, cewa an nuna wani samfurin kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen spananci daga cikin manyan ayyukan da babba mamalimn addinin mulunci Ayatollah Shirazi ya gudanar wanda kuma ake lissafa shi a cikin manyan tafsirai na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbaba agare shi a da iylan gidansa a wannanzamani da muke ciki.
A wani labarin kuma jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya daura alhakin gurgunta shirin wanzar da zaman lafiya a kasar Siriya kan kasashen yammacin Turai. A jawabin da ya gabatar a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya; Is'hak Ali-Habib jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan kokarin da kasashen yammacin Turai ke yi na yin kafar ungulu ga shirin warware rikicin kasar Siriya da Kofin Annan ya gabatar, domin shirin yana neman warware rikicin kasar ta Siriya ne ta hanyar lumana.
Ali-Habib ya kara da cewa; mafi yawan daftarin kudirin da kasashen yammaci ke gabatarwa kan kasar Siriya, kudiri ne da ke neman tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan Siriya, lamarin da zai kara ruruta wutar tashe tashen hankula da rikici a kasar, kuma wasu daga cikin daftarin kudurin da suke gabatarwa kan kasar ta Siriya su suka janyo har aka samu kafar aikewa da makamai da kudade ga 'yan ta'addan kasar.
1069806




captcha