IQNA

Mafi Karantar Kwafin Kur’ani Mai tsarki A Taron Baje Kolin Kasa Da Kasa

17:48 - August 04, 2012
Lambar Labari: 2385251
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani karamin kur’ani mafi tsarki wanda shi ne mafi karanta da aka taba nunawa a wajen wannan taron baje koli da aka fara tun farkon watan Ramadan mai alfarma a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci a karo na ashirin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo bangaren yada labaransa na cikin gida, cewa an nuna wani karamin kur’ani mafi tsarki wanda shi ne mafi karanta da aka taba nunawa a wajen wannan taron baje koli da aka fara tun farkon watan Ramadan mai alfarma a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci a karo na ashirin, kuma ana samun ci gaba ta wannan fuska matuka.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar matsin lambar da wasu kasashen yammaci suke yi wa a kan Iran ba zai taba raunana al'ummar Iran din da kuma tilasta musu sauya tafarkin da suka rika ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi a yammacin jiya da wasu gungun masana da jami'an cibiyoyin ilimi na Iran inda ya ce al'ummar Iran dai sun kuduri aniyar kai wa ga kololuwar ci gaba ta hanyar tsayin daka da kuma karfin gwuiwa, don haka babu wani abin da ya isa ya shiga tsakaninsu da wannan manufa da suka sa a gaba.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da irin matsin lamba da makirce-makirce na tattalin arziki da ake kulla wa Iran da kuma irin farfagandar da ake yadawa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran duk dai da nufin raunana ruhin al'ummar kasar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: al'ummar dai a tsaye suke sannan kuma matsaloli da matsin lambar da ake musu sun gaza wajen raunana iradar su. Kafin jawabin Jagoran dai wasu daga cikin masanan sun gabatar da mahangarsu kan lamurra daban-daban da suka shafi Iran da yanayi da take ciki.
1069869






captcha