IQNA

Musulmin Palastinu Sun Samu Damar Gudanar Da Sallar Juma’a A Qods

17:49 - August 04, 2012
Lambar Labari: 2385253
Bangaren kasa da kasa, sama da mutane dubu dari uku ne suka halarci sallar juma’a da aka gudanar a masallacin Qods mai alfarma a juma ata uku a watan Ramadan mai alfarma bayan da sojojin yahudawa da kuma masu tsattsauran ra’ayi daga cikin yahudawan suka hana musulmi shiga cikin masallacin domin yin ibada.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ittihad ta kasar hadaddiyar daular larabawa, cewa sama da mutane dubu dari uku ne suka halarci sallar juma’a da aka gudanar a masallacin Qods mai alfarma a juma ata uku a watan Ramadan mai alfarma bayan da sojojin yahudawa da kuma masu tsattsauran ra’ayi daga cikin yahudawan suka hana musulmi shiga cikin masallacin domin yin ibada kamar yadda suka daba yi a kowace juma’a.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauki matakin takura ma palastinawa domin hana su gudanar da tarukan addini da suka saba yi a a cikin masallacin a lokacin azumin watan Ramadan, uwa uba kuma ga lokacin gudanar da zanga-zangar ranar Qods na ci gaba da karatowa wadda take a matsayin wata babbar barazana ga haramtacciyar kasar yahudawan.
Rahoton ya tabbatar da cewa sama da mutane dubu dari uku ne suka halarci sallar juma’a da aka gudanar a masallacin Qods mai alfarma a juma ata uku a watan Ramadan mai alfarma bayan da sojojin yahudawa da kuma masu tsattsauran ra’ayi daga cikin yahudawan suka hana musulmi shiga cikin masallacin domin yin ibadar salla da sauran ayyuka.
1070084

captcha