IQNA

Wani Matasghi Dan Shekaru Tara Yana Halartar Gasar Kur’ani Ta Birnin Dubai

11:21 - August 05, 2012
Lambar Labari: 2385721
Bangaren kasa da kasa, wani matashi dan shekaru tara ya halarci gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Dubai fadar mulkin kasar hadaddiyar daular larabawa inda ya taka gagarumar rawa kuma ya burge dukkanin mahalrta gasar da suke wakiltar cibiyoyin addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran wam, cewa wani matashi dan shekaru tara ya halarci gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Dubai fadar mulkin kasar hadaddiyar daular larabawa inda ya taka gagarumar rawa kuma ya burge dukkanin mahalrta gasar da suke wakiltar cibiyoyin addinin muslunci da suke cikin kasashen musulmi da na larabawa.
A wani labarin kuma na dama jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar matsin lambar da wasu kasashen yammaci suke yi wa a kan Iran ba zai taba raunana al'ummar Iran din da kuma tilasta musu sauya tafarkin da suka rika ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi a yammacin jiya da wasu gungun masana da jami'an cibiyoyin ilimi na Iran inda ya ce al'ummar Iran dai sun kuduri aniyar kai wa ga kololuwar ci gaba ta hanyar tsayin daka da kuma karfin gwuiwa, don haka babu wani abin da ya isa ya shiga tsakaninsu da wannan manufa da suka sa a gaba.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da irin matsin lamba da makirce-makirce na tattalin arziki da ake kulla wa Iran da kuma irin farfagandar da ake yadawa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran duk dai da nufin raunana ruhin al'ummar kasar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: al'ummar dai a tsaye suke sannan kuma matsaloli da matsin lambar da ake musu sun gaza wajen raunana iradar su. Kafin jawabin Jagoran dai wasu daga cikin masanan sun gabatar da mahangarsu kan lamurra daban-daban da suka shafi Iran da yanayi da take ciki.
1070892

captcha