Bangaren kasa da kasa, marigayi Imam Khomeini (RA) shi ne babbar gadar da ta hada jami’a da kuma cibiyoyin ilimi na Huza domin haduwa da kuma kusanto fahimtar juna saboda a hadu a yi wa addinin muslunci da kuma al’ummar musulmi aiki tatre da takawa makiyan muslunci birki.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na cikin gida cewa, Sheikh Muhammad Iraki ya bayyana cewa marigayi Imam Khomeini (RA) shi ne babbar gadar da ta hada jami’a da kuma cibiyoyin ilimi na Huza domin haduwa da kuma kusanto fahimtar juna saboda a hadu a yi wa addinin muslunci da kuma al’ummar musulmi aiki tatre da takawa makiyan muslunci birki kan shishigin da suke kan Musulunci da kuma musulmi.
Ko shakka babu kamar yadda ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar yahudawa sahyuniya ya bayyana ne a ziyarar da ya kai Amurka a watan Fabrairun da ya wuce don neman goyon bayan Amurka kan amfani da karfi a kan Iran inda ya ce haramtacciyar kasar yahudawa sahyuniya tana da zabi daban-daban wajen fada da shirin nukiliyan na Iran. Duk da cewa batun kawo hari kan Iran ba abu ne mai sauki ba a gare su sakamakon abin da zai biyo bayan hakan, to amma ko shakka babu amfani da hanyar barazana da kisan gillan suna daga cikin hanyoyin da suka dauka don cimma bakar aniyarsu kan Iran.
Akwai shaidu da yawan gaske da suke nuni da yadda kungiyar leken asirin haramtacciyar kasar yahudawa sahyuniya ta yi amfani da wannan hanya ta kisan gilla don ciyar da manufar haramtacciyar kasar yahudawa sahyuniya gaban. A 'yan watannin da suka gabata ma dai jaridar Sunday Telegraph ta Birtaniya ta buga wani labara da ke nuni da hannun kungiyar leken asirin haramtacciyar kasar yahudawa sahyuniya cikin kisan gillan da aka yi wa masanan na Iran cikin shekaru biyun da suka gabata. Ko shakka babu abubuwan da wadannan 'yan jarida suka fadi cikin wannan littafi nasu wani abu ne da ke nuni da asalin tushen wannan haramtacciyar kasar wacce ta ginu bisa kisan gilla da ayyukan ta'addanci.
1070425