Bangaren kasa da kasa, ana yin gyra da kwaskwarima ga babban mushafin na kasar hadaddiyar daular larabawa wanda a kowace shekara a kan fitar d shia wurin gasar karatu da hardar kur’ani da ae gudanarwa a kasar da ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya da dama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wam, cewa ana yin gyra da kwaskwarima ga babban mushafin na kasar hadaddiyar daular larabawa wanda a kowace shekara a kan fitar d shia wurin gasar karatu da hardar kur’ani da ae gudanarwa a kasar da ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya da dama, musamman ma kasashen musulmi da na larabawa.
Dangane da halin da musulmi suke ciki kuwa taron kasa da kasa da aka gudanar a kasar Malesiya ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar musulmi a kasar Myanmar wato "Bama". Taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malesiya a jiya juma'a ya bayyana kisan gillar da ake yi wa musulmai a kasar Myanmar musamman a jihar Rakhine da cewar take hakkin bil-Adama ne da ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.
Daukacin mahalatta zaman taron sun kuma bukaci daukan matakin matsin lamba kan gwamnatin Myanmar domin ta bada izini ga kungiyoyin kasa da kasa musamman kungiyar hadin kan kasashen musulmi don su kai taimakon gaggawa ga musulmin da suke cikin muwuyacin hali. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ce ta bukaci gudanar da zaman taron, kuma kungiyoyin kasa da kasa kimanin 30 ciki har da Majalisar Dinkin Duniya ne suka halacci taron na kasa d akasa.
1070608