IQNA

Samun Masaniya Tsakanin Makaranta Kur’ani Na Daga Cikin Mnaufofin Gasar Dubai

17:14 - August 06, 2012
Lambar Labari: 2387024
Bangaren kasa da kasa, samun masaniya tsakanin maaranta da mahardata kur’ani mai tsarki daga kasashen duniya na daga cikin manufofin gudanar da gasar karatun kur’ani da kuma harda a birnin Dubai da kuma masu halartar gasar domin ganewa idanunsu yadda ake gudana saboda kaunarsu da kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, bangaren yada labaransa na yankin gabas ta tsakiya ya habarta cewa , samun masaniya tsakanin maaranta da mahardata kur’ani mai tsarki daga kasashen duniya na daga cikin manufofin gudanar da gasar karatun kur’ani da kuma harda a birnin Dubai da kuma masu halartar gasar domin ganewa idanunsu yadda ake gudana saboda kaunarsu da kur’ani mai tsarki kamr dai yadda suka saba kowace shekara.
Wanann gasar dai ana gudanar da ita a karo an goma sha shida a birnin Dubai, wadda ake lissafa ta a matsayin daya daga cikin masu matukar muhimamnci da ake gudanarwa a cikin kasashen larabawa na yanakin gabas ta tsakiya, kuma ko shakka babu hakan zai taimaka matuka wajen karafafa gwiwar masu sha’awar karatu da hardar kur’ani mai tsarki.
Ya ci gaba da cewa an girmama wasu cibyoyi da suke gdanar da ayyuka na jin kai a cikin kasashen musulmi dana larabawa bisa la’akari da ayyuan da suke gudanarwa wanda yake amfanar da mabiya addinin muslunci a sassa na kasashensu kamar yadda har ma wasu da ba musulmi suna samun irin wannan taimako wanda kungiyoyin suke bayarwa musamman ga mabukata. 1071860
captcha