IQNA

An Nuna Shakku Dangae Da Kwarewa A Alkalancin Gasar Karatun Kur’ani Ta Dubai

12:46 - August 07, 2012
Lambar Labari: 2387642
Bangaren kasa da kasa, mahaifi kuma wanda ya raka Muhammad Madj makarancin kur’ani dan kasar Iran zuwa gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya da aka gudanar a birnin Dubai cibiyar kasawancin hadaddiyar daular larabawa ya bayyana cewa akwai karancin masaniya kan yadda ake gudanar da alkalancin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa ayankin gabas ta tsakiya, cewa mahaifi kuma wanda ya raka Muhammad Madj makarancin kur’ani dan kasar Iran zuwa gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya da aka gudanar a birnin Dubai cibiyar kasawancin hadaddiyar daular larabawa ya bayyana cewa akwai karancin masaniya kan yadda ake gudanar da alkalancin gasar kur’ani a matsayi na duniya irin wannan.
cewa sakamakon gagarumar gudunmawar da kamfanin dillanncin labaran iqna ya bayar wajen daukar hotuna da bayar da labarai cikin sauri kan gasar karatu da ahardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Dubai fadar kasuwancin kasar hadaddiyar daular larabawa an bayar da kyutar giramawa gare shi saboda kokarin da ya yi, kamar yadda masu shirya gasar suka sanar.
A wani labarin kuma jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bada labarin shirya zaman tattaunawa kan matsalar Siriya domin warware rikicin kasar ta hanyar lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren alaka da kasashen Larabawa da nahiyar Afirika Husaini Amir Ilahiyon a yau litinin ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata karbi bakoncin kasashen da suke adawa da duk wani shirin daukan matakin soji kan kasar Siriya, kuma suke bibiyar hakikanin abin da ke faruwa a kasar ta Siriya, don gabatar da shawarwari kan hanyar warware rikicin kasar ta hanyar lumana a kasar.
1071576


captcha