IQNA

Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa A masar Karo Na Ashirin A Cikin Wannan Mako

12:45 - August 07, 2012
Lambar Labari: 2387643
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a karo na ashirin a kasar Masar tare da halartar masana daga sassa na kasashen musulmi da na larabawa kamar dai yadda bangaren hulda da jama’a na cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka dai ana shirin fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a karo na ashirin a kasar Masar tare da halartar masana daga sassa na kasashen musulmi da na larabawa kamar dai yadda bangaren hulda da jama’a na cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki da kuma shirya gasa.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani labarin kuma jami’an tsaron kasar Masar na ci gaba da killace wurin da aka kai hari a jiya da ke kan iyakar kasar da yankunan palastinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye, wanda yay i sanadiyar mutuwar dakarun Masar 16.
Jim kadan bayan kai harin na jiya shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya kira taron gaggawa tare da majalisar tsron kasar domin tattauna batun, wani bayanin da ya fito daga ofishin shugaban ya kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ba za ta bari wannan lamarin ya wuce ba tare da daukar matakan da suka dace ba.
Kungiyar Hamas a Palsdinu ta bayyana cewa bata da hannu a cikin wannan harin kuma ta toshe dukkan ramukka masu shigowa yankin domin hana wadanda suke da hannu kan kisan shigowa yankin. 1072019




captcha