Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alwasat ta kasar Bahrain, cewa za a gudanar da taron kammala gasar karatun kur’ani mai tsarki da harda a kasar Bahrain tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar kamar dai yadda aka saba gudanarwa a cikin kowane watan azumin Ramadan mai alfarma a kasar.
A bangare guda kuma rahotanni daga kasar Bahrain sun habarta cewa, jami’an tsaron kasar sun afka kan yankuna da dama domin murkushe fararen hula masu neman sauyi na siyasa a kasar ta hanayar lumana.
Rahotannin sun tabbatar da cewa jami’an tsaron na kasar Bahrain sun kai hari a kan yankuna da garuruwa 19 a cikin daren jiya, inda suka yi ta harba hayaki mai sanya hawaye mai dauke da sanadaran guba, gami da harsasan chozen da aka haramta yin amafani da su a bisa dukkanin dokoki na duniya.
Wasu rahotanni da jaridar New York Times ta buga sun tabbatar da cewa, yanzu haka sojojin Amurka 240 sun kammala shiri domin isa kasar Bahrain, da nufin kare masarautar kasar daga boren al’umma, da kuma taimaka ma jami’an tsaro wajen murkushe masu zanga-zangar lumana.
1072294