IQNA

Masana Yakin Kwakwalya Su Mayar da Martani Kan Makiya Ta Hanyar Da Ta Dace

9:52 - August 08, 2012
Lambar Labari: 2388107
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci ya fadi a gaban dubban daliban jami'a cewa, ya zama wajibi kan duk wadanda suke da masaniya kan hanyoyi na sadarwa da kuma yakin kwakwalya das u yi amfani da dukaknin abin da yake hannunsu wajen fuskantar makircin makiya ta hanoyin da suka da ce.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na na jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran, cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wasu malaman adabin farisanci da matasa mawaka don tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Hasan al-Mujtaba (a.s). A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a wajen taron, Jagoran ya yi ishara da irin ci gaban da mawaka suke samu a Iran cikin karamin lokaci yana mai cewa: Ci gaba da wannan yunkuri, zai ba wa kasar mu mai girma wata dama ta sake gabatar wa al'adu da ci gaban duniya musamman wannan yankin wata kyauta ta daban.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Waka dai ba ya ga cewa wata dama ce da mawaki zai bayyanar da irin tunani da yadda yake ji, haka nan kuma wajibi ne ta zamanto wajen hidima da ci gaban ababe masu kima. A saboda haka wajibi ne mawaki a matsayin sauke nauyin da ke wuyansa ya yi amfani da wannan ni'ima ta Ubangiji wajen hidima ga addini, kyawawan halaye, juyin juya halin Musulunci da masaniya ta Ubangiji.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wake yana iya yin hidima da taimakawa masaniya ta addini da kyawawan halaye na mutane da kuma yunkuri na juyi na al'umma. Yana iya yin hakan kuwa hatta ta hanyar baiti guda ko baitoci biyu na waken juyin da kyawawan halaye da masaniya ta Ubangiji. Hakan yana iya yin tasirin gaske.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin tasirin da murya da kuma abin da waka ta kumsa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Bai kamata mawaka su nuna halin ko in kula dangane da yanayi da abubuwan da ke faruwa a kasar Iran ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana gagarumin zaluncin da ake yi wa Iran a fagen shirin makamashin nukiliyanta da kuma kashe wasu daga cikin masanan kasa a matsayin daya daga cikin misalan hakikanin lamurran da ke faruwa a Iran inda ya ce: Ma'abota girman girman kan da dukkanin karfinsu na farfaganda da kafafen watsa labarai da bangare na siyasa sun tsaya kyam wajen fada da al'ummar Iran, sannan kuma al'ummarmu tana ci gaba da tsayin daka. A saboda haka bai kamata mawakanmu su rufe ido kan wadannan lamurra ba. Don kuwa babu yadda mutum zai zamanto dan ba ruwanmu a fagen fada tsakanin karya da gaskiya.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da yadda wasu su ka zamanto ‘yan ba ruwanmu dangane da lamurran da suka shafi kallafaffen yaki da mamayan makiya da sunan nuna kwarewa ta aiki, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Amma sai ga shi wadannan mutanen suna yada tunani da akidu na fada da addini da kyawawan halaye da manyan batutuwa na kasa da kuma juyin juya halin Musulunci, alhali kuwa babu wani abin da suka nuna wajen fada da makiya.
A karshen jawabin nasa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kirayi mawakan da cewa: mutanen da suke gudanar da ayyukansu da kuma yin hidima ga bangaren gaskiya da koyarwa ta Ubangiji, wajibi ne a koda yaushe su zamanto masu kula da kansu sannan kuma su ci gaba da tsayin daka a kan wannan tafarkin.
Tun da farkon ganawar dai, sai da wasu daga cikin mawakan suka gabatar da wakokinsu da suka shafi bangare na addini, juyin juya halin Musulunci, zamantakewa ta al'umma da kuma irin farkawa da al'ummar musulmi suke ci gaba da samu.
1072741
captcha