IQNA

An Yi Kira Da A dauki Tsauraran Matakai Kan gwamnatin Kasar Myanmar A Pakistan

12:17 - August 08, 2012
Lambar Labari: 2388327
Bangaren kasa da kasa, an yi kira da adauki matakan da suka dace kan gwamnatin kasar Myanmar dangane da kisan kiyashin da take yi wa mabiya addinin muslunci na kasar kamar dai yadda duniya ta sheda duk kuwa da cewa kasashen da suke raya kare hakkin bil adama a duniya bas u uffan ba kan hakan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar The News, cewa wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kira da adauki matakan da suka dace kan gwamnatin kasar Myanmar dangane da kisan kiyashin da take yi wa mabiya addinin muslunci na kasar kamar dai yadda duniya ta sheda duk kuwa da cewa kasashen da suke raya kare hakkin bil adama a duniya bas u uffan ba kan hakan, tare da cewa kasar ta yi hakan ne da gangan.

A cikin watannin bayan nan, musulmin kasar Mayammar sun zama karen gwajin dafi na nuna kin jiki da tsangwana. Mabiya addinin Budda masu tsattsauran ra'ayi a yankin Rakhtin da ke yammacin kasar suna yi wa musulmin kisan gilla saboda kawai su musulmi ne. Ita kuwa gwamnatin kasar ta sanya ido tana kallon abinda ya ke faruwa ba tare da dauki matakin da ya dace ba. Har ila yau, kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama a duniya sun yi gum da bakunansu kai kace wadanda ake kashewa ba bil'adama ba ne da su ke riya cewa suna karewa hakki.

Kawo ya zuwa yanzu lamirin duniya bai girgiza ba akan kisan da ake yi wa musulmin mayyamar da kona gidajensu da shagunansu na kasuwanci. Babu wanda ya zubar da koda hawaye akan musulmi dubu dari takwas da rayuwarsu ta ke fuskantar bakar wahala. Shin saboda mutanen da ake kashewa a muyammar musulmi ne, ko kuma saboda tsiraru ne? Yadda al'amurra su ke tafiya a cikin kasar ta Muyammar a yanzu na nuni da cewa za a ci gaba da samun asarar rayuka anan gaba, tunda dai babu alamar za a takawa masu makasa birki. Ga dukkanin alamu'kisan da 'yan budda su ke yi wa musulmi a cikin Muyammar suna yi ne da tallafin gwamnatin kasar. Su ke kuma korarsu daga gidajensu da maida su zama 'yan gudun hijira na tilas.

1072990







captcha