IQNA

A Ci Gaba Da Keta Hurumin Musulmin Kasar Myanmar An Kone Daya Daga Cikin Masallatansu

11:10 - August 11, 2012
Lambar Labari: 2389916
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da keta hurumin musulmin kasar Myamnar da mabiya addinin buda gami da jami’an tsaron gwamnatin kasar suke yi a jiya a n kone daya daga cikin manyan masallatai mallakin musulmin kasar ba tare da duniya ta ce uffan kan hakan ba.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa a wani mataki na ci gaba da keta hurumin musulmin kasar Myamnar da mabiya addinin buda gami da jami’an tsaron gwamnatin kasar suke yi a jiya a n kone daya daga cikin manyan masallatai mallakin musulmin kasar ba tare da duniya ta ce uffan kan hakan ba kamar dai yadda rahotanni suka tabbatar.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Bangaladesh da ta bada izinin shigar da kayayyakin jin kai ga 'yan gudun hijiran kasar Myanmar da suke cikin kasarta. A sakon bayanin da Majalisar Dinkin Duniya ta aike ga gwamnatin Bangaladesh a jiya talata ta bukaci gwamnatin kasar ta Bangaladesh da ta amince wa kungiyoyin kasa da kasa su shiga cikin kasarta domin gabatar da taimakon jin kai ga 'yan gudun hijirar Myanmar.
Dubban musulmi 'yan kasar Myanmar ne suke cikin kasar Bangaladesh bayan da suke tsere daga mahallinsu sakamakon kisan kiyashin da 'yan addinin Buoza da jami'an tsaron Myanmar ke musu, kuma gwamnatin Bangaladesh ta hana kungiyoyin kasa da kasa shiga cikin kasarta domin gabatar musu da taimako bisa da'awar cewa; musulmin Myanmar din sun shiga cikin kasarta ne bada izini ba, sakamakon haka rayuwar dubban musulmin Myanmar da suke sansanonin da aka kebe musu a kasar ta Bangaladesh ke cikin hatsari.
1075280






captcha