IQNA

Yan Majalisar Masar Sun Ki Amincewa Da Buga Wani Kur’ani Mai Juzu’I 28

11:10 - August 11, 2012
Lambar Labari: 2389918
Bangaren kasa da kasa, yan majalisar dokokin kasar Masar sun ki amincewa da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka shirya shi a cikin juzu’I 28 wanda suke ganin cewa yin hakan tamkar rage kimars ane da kuma haifar da wata sunna da sabawa abin da ak asania a cikin addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit cewa, wasu daga cikin yan majalisar dokokin kasar Masar sun ki amincewa da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka shirya shi a cikin juzu’I 28 wanda suke ganin cewa yin hakan tamkar rage kimars ane da kuma haifar da wata sunna da sabawa abin da ak asania a cikin addini saboda haka, suka yi watsi da wannan batu baki daya.
A wani labarin na daban kuma ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewa: Gwamnatin Masar zata sanya kafar wando daya da duk wani mai neman yin zagon kasa ga zaman lafiyar kasar. A bayanin da ministan harkokin wajen kasar Masar Muhammad Amru ya fitar a yau juma'a yana dauke da cewa: Gwamnatin Masar ba zata taba lamuntar duk wani zagon kasa ga zaman lafiyar tsibirin Sina ko duk wani yankin kasar Masar ba, kuma zata dauki kwararan matakai kan duk wata barazana ga zaman lafiyar kasar.
Ministan na harkokin wajen Masar Muhammad Amru ya kuma jaddada cewa; jami'an Masar sun zage dantse wajen warware duk wata matsalar tsaro a tsibirin Sina, saboda tabbatar da zaman lafiya da tsaro sune kan gaba a ayyukan da sabuwar gwamnatin kasar ta runguma.
1074961
captcha