IQNA

An Gudanar Da Taron Raya Daren Lailatul Qadr A Birnin Paris Na Kasar faransa

17:29 - August 11, 2012
Lambar Labari: 2390348
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron raya daren lailatul Qadr a birnin Paris na kasar Faransa tare da halartar daruruwan musulmi da suke zaune a kasar da suka hada kuma da baki yan kasashen larabawa da na suulmi inda suka gudanar da ibada da kuma addu’oi da suka kebanci wannan dare mai daraja da alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bait Zahra, cewa an gudanar da taron raya daren lailatul Qadr a birnin Paris na kasar Faransa tare da halartar daruruwan musulmi da suke zaune a kasar da suka hada kuma da baki yan kasashen larabawa da na suulmi inda suka gudanar da ibada da kuma addu’oi da suka kebanci wannan dare mai daraja da ke cikin wannan wata na Ramadan.
Bayanin ya kara da cewa cibiyar bunkasa al’adu da ilimin muslunci ta kasar faransa tana jiran samun taimako daga musulmin kasar dangane da ayyukan da take gudanarwa na kara yada ilmomin musunci a kasar bayan samun cikakken goyon baya daga kungiyoyin musulmin kasar wadda day ace daga cikin kasashen yammacin turai.
Babbar cibiyar mabiya addinin muslunci ta Tauhid da ke da babban ofishin a birnin Paris tan adaukar nauyin shirya taron buda baki ga mabiya addinin muslunci da suke zaune a cikin birnin kamar dai yadda bangaren hulda da jama’a na cibiyar ya sanar a cikin wani bayani da ta fitar ta hanyar yanar gizo.
Wannan cibiya dai tana cikin uhimman cibiyoyi na mabiya addinin muslunci da suke gudanar da ayyukansu a kasar faransa da nufin kara fadada fahimtar mutanen kasar dangane da addinin muslunci, da kuma yi was u kansu musulmin hannunka mai sanda kan addininsu kasantuwar suna rayuwa a cikin wata kasa da babu ruant da addinin musucnci kuma, al’ummarta suna fada da shi.
1074972




















captcha