IQNA

An Yi Kira Da A Saki Babban Malamin Nan Na Kasar Saudiyya Da Ake Tsare Da Shi

17:29 - August 11, 2012
Lambar Labari: 2390349
Bangaren kasa da kasa, kungiyar afuwa ta duniya ta yi kira ga mahukuntan kasar Saudiyya da su yi hukunci a kansa ko kuma agaggauta sakinsa daga gidan kason da ake tsare da shi ba tare da wani dalili ko wata hujja ta yin haka ba duk kuwa da cewa bayanai sun tabbatar da cewa yana cikin halin na rashin lafiya sakamakon harbinsa da bindiga da aka yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa kungiyar afuwa ta duniya ta yi kira ga mahukuntan kasar Saudiyya da su yi hukunci a kansa ko kuma agaggauta sakinsa daga gidan kason da ake tsare da shi ba tare da wani dalili ko wata hujja ta yin haka ba duk kuwa da cewa bayanai sun tabbatar da cewa yana cikin halin na rashin lafiya sakamakon harbinsa da bindiga da aka yi a lokacin da jami’an tsaron masarautar Saudiyya suka je kame shi.
Tun a cikin watan da ya gabata ne dai mahukuntan wahabiyawan Saudiyya suka kame sheikh Namir bisa zarginsa ta tuinzura jama’a domin su nuna kyama ga gwamnatin Ali-Saud da ke mulkin fir’ananci a kasar tsawon shekaru sama da dari daya, duk kuwa da cewa bat aba jarraba mulkin demokradiyya akasar ba, amma dai duk da haka suna samun goyon bayan Amurka da yahudawan sahyuniya.
Kungiyar afuwa ta duniya ta yi kira ga mahukuntan kasar Saudiyya da su yi hukunci a kansa ko kuma agaggauta sakinsa daga gidan kason da ake tsare da shi ba tare da wani dalili ko wata hujja ta yin haka ba duk kuwa da cewa bayanai sun tabbatar da cewa yana cikin halin na rashin lafiya sakamakon harbinsa da bindiga da aka yi a cikin watan da ya gabata. 1074968



















captcha