Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen bangaren baje kolin kayayyakin kur’ani na kasa da kasa wanda ak gudanarwa a bbabn masallacin birnin Tehran tun daga farkon watan ramadan mai alfarma amma kuma bangaren cikin gida na ci gaba da gudanar da nasa baje kayyakin na kur’ani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa an kawo karshen bangaren baje kolin kayayyakin kur’ani na kasa da kasa wanda ak gudanarwa a bbabn masallacin birnin Tehran tun daga farkon watan ramadan mai alfarma amma kuma bangaren cikin gida na ci gaba da gudanar da nasa baje kayyakin na kur’ani mai tsarki.
Jagororin mabiyan addinan kiristanci da muslunci a yankin Jubail na kasar Lebaon sun gana a babban ginin majami’ar Sin Jan da ke yankin dangane muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu da za su taimaka wajen kara samun fahimtar juna a tsakaninsu.
Taron tsakanin bangarorin biyu ya gamsar da masu halatarsa, bisa la’akari da irin yadda kasar Lebanon ta zama wurin buga misali na fahimtar juna tsakanin mabiya addinan kirsitanci da muslunci, duk kuwa da yakin basasa da bangarorin biyu suka yi a lokutan baya wanda aka jaza musu da nufin wargaza su, amma kuma hakan sai ya zama wani dalili na hada kansu.
Manyan jagororin mabiyan addinan kiristanci da muslunci a yankin Jubail na kasar Lebaon sun gana a babban ginin majami’ar Sin Jan da ke yankin dangane muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu da za su taimaka wajen kara samun fahimtar juna. 1076673