Bangaren kasa da kasa, an yi bayani kan hanyoyi mafi sauki wahen gudanar da hardar kur’ani mai tsarki a makarantun kur’ani mai tsarki na kasar Senegal wanda ake yin amfani da wannan sabon tsari a wasu kasashen da suka samu gagarumin ci gaba da fuskacin harkokin kur’ani mai tsarki kamar dai yadda daya daga cikin mahalarta taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa ya fada a jiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaran, an yi bayani kan hanyoyi mafi sauki wahen gudanar da hardar kur’ani mai tsarki a makarantun kur’ani mai tsarki na kasar Senegal wanda ake yin amfani da wannan sabon tsari a wasu kasashen da suka samu gagarumin ci gaba da fuskacin harkokin kur’ani mai tsarki kamar dai yadda daya daga cikin mahalarta taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa ya fada a jiya a gaban mahalarta taron.
A cikin kwanakin nan an fara gudanar da wani shiri na koyar da kur’ani mai tsarki a cikin makarantun gwamnati a kasar Senegal wanda zai kasance bisa hanyoyi na zamani ta yadda dalibai za su iya koyon karatu da rubutun kur’ani mai tsarki a saukake domin karfafa addinin muslunci da fahimtar koyarwarsa a tsakanin matasan kasar da ke yammacin nahiyar Afirka.
Bayanin ya ci gaba da cewa sabuwar gwamnatin kasar ta Senegal ce ta bullo da wannan shiri, bayan da ma’aikatar kula da harkokin addini ta mika shawara ga gwamnati kan hakan kuma aka amince da shawar, inda yanzu malaman addini da suke koyarwa a makarantun gwamnatin Masar suka fara samun hoo domin gudanar da wanna shiri yadda ya kamata, kuma ana sa ran shirin zai kankam ne a cikin shekara ta dubu biyu da goma sha uku.
1076167